Alaka tsakanin Blair da Gordon Brown

Bangon littafin Firayim Minista Tony Blair
Image caption Blair ya ce hulda da Gordon Brown na da wahala

Wani banagare na littafin da Tony Blair ya wallafa a kan rayuwarsa ya ambato tsohon Firayim Ministan Burtaniyar yana cewa Gordon Brown ba zai iya kai jam'iyyar Labour ga nasara ba.

Bangarorin littafin da kuma hirarrakin da aka wallafa a jaridu dai sun yi nuni da tsattsamar dangantaka tsakanin tsohon Firayim Ministan da ministansa na kudi a tsawon lokacin da Tony Blair ya yi yana mulki.

Mista Blair ya ce hulda da Gordon Brown na da matukar wahala da kuma rikitarwa to amma, a cewarsa, ya kyale Gordon Brown din a mukaminsa ne saboda gara ya kasance a killace da a bar shi ya yi abin da ransa ya ke so.

Da ya ke magana a kan zaman Gordon Brown a kan mukamin Firayim Minista ne Mista Blair ya ce ba abu ne da zai yi nasara ba.

Ya ce jam'iyyarsu ta fadi a zaben 2010 ne saboda ta kaucewa akidunta na sabuwar Labour.

Dangane da yakin Iraki kuwa cewa ya yi bai iya tsinkayar mummunan tashin hankalin da zai biyo bayan mamaye kasar ta Iraki ba.

Mista Brown ya jaddada takaicinsa dangane da asarar rayukan da aka tafka.

Sai dai yayin da ya ke cewa yana tausawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a Irakin ya kuma ce ba zai nemi gafara saboda shawarar da yanke ta shiga yakin ba.