Joe Biden ya tabbatar za a kafa sabuwar Gwamnati a Iraqi

Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden, ya ce, yayi imanin cewa 'yan siyasar Iraqi na gab da amincewa da kafa wata sabuwar gwamnati.

Mr Biden yana Iraqi domin halartar bukin kawo karshen aikin dakarun Amurka a fagen daga.

Ya shaidawa gidan talabijin din Amurka na CBS cewa ya gana tare da shugabannin dukkanin bangarorin siyasar kasar a lokacin ziyarar tasa, kuma ya gamsu cewa nan ba da jimawa ba za su iya kafa gwamnati.

Ya ce "aikin yantar da Iraqi ya kawo karshe. To amma alakar Amurka da Iraqi zai ci gaba, inda za a fara wani sabon aiki a yau, mai suna Operation New Dawn".