Mahukuntan Palasdinawa sun kama yan kungiyar Hamas

Mahmoud Abbas, Shugaban Palasdinawa
Image caption Mahmoud Abbas, Shugaban Palasdinawa

Mahukunta a Palasdinu sun kaddamar da daya daga cikin aikin tsaro mafi girma a kan abokan adawarsu na Hamas, bayan da mayakan Hamas din suka halaka Yahudawa 'yan kama wuri zauna guda hudu a gabar yammacin kogin Jordan.

Harin ya zo ne ana gab da fara tattaunawa ta kai tsaye tsakanin Israela da Palasdinawa a Washington wanda aka dade ana jiran gani.

Ministan tsaron Isra'ila Ehud Barak yayi kira da a kai zuciya nesa.

Ya ce "ina fata za mu iya dakatar da irin wannan sabon nau'i na hare haren ta'addanci wanda aka yi domin gurgunta tattaunawar sasantawar da ake farawa yau a Washington".