Dashen koda a asibitin Jami'ar Maiduguri

Abubakar Usman
Image caption Abubakar Usman wanda ya bayar da kodar sa gudumawa tare da wakiliyar BBC Bilkisu Babangida

A Najeriya a karon farko Asibitin Koyarwa na Jami'ar Maiduguri ya gudanar da aikin tiyatar dashen koda shekaru goma sha bakwai bayan da aka kafa cibiyar lura da masu cutar kodar na shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Kwararrun likitoci ne daga Asibitocin Koyarawa na Mallam Aminu Kano da na Obamefemi Awolowo suka halarci wannan aikin tiyata domin tallafa wa takwarorinsu na Jami'ar Maidugurin inda suka samu nasarar yi wa mutum guda wanda ya samu gudunmawar kodar daga dan unwansa da yanzu haka suke kwance a asibitin suna murmurewa.

Cutar kodar dai aba ce da ke ci gaba da hallaka daruruwan jama'a a kasashe da dama musamman masu tasowa sakamakon tsadar jinya da rashin isassun kwararru da kayan aikin a asibitoci.

Bayan shekaru bakwai da kaddamar da Cibiyar Lura da masu Cututtukan da suka shafi kodar ne aka fara gudanar da aikin jinyar tace jini ga daruruwan masu cutar domin saukaka tafiyar da rayuwar su.

Sauyi wajen fita jinya

Farfesa Othman Kyari, Babban Daraktan Asibitin Koyarwa na Jami'ar Maiduguri ya bayyana cewa, dashen koda na farko a asibitin, wanda ya samu hadin kan kwararrun daga Asibitocin Koyarwa na Malam Aminu Kano da Obafemi Awolowo zai iya kawo sauyi wajen fita jinyar da wasu masu fama da cutar ke yi zuwa kasashen waje, da kuma masu karamin karfi zasu iya samun saukin jinya.

Dokta Williams Wudiri daya daga cikin kwararun da suka gudanar da aikin tiyatar ga Abubakar Usman mai shekaru 27 da haihuwa, wanda ya sadaukar wa da yayansa Suleiman Usman dan shekaru 31 da haihuwa kodarsa daya, ya bayyana cewar majinyacin ya shafe kimanin shekaru biyu yana jinyar tace jini a asibiti.

Image caption Abubakar Usman na farin cikin da taimakawa dan uwansa.

Ya kuma kara da cewa wannan shi ne karon farko da aka gudanar da aikin dashen koda a Najeriya ba tare da an gayyato kwararru daga kasashen waje ba, wanda ya nuna alamun cewar za a samu saukin kashe kudaden da akan yi wajen jinya. Abubakar Usman ya bayyana godiyar sa ne ga Allah da ya bashi karfin gwiwar da ya samu na ceton rayuwar dan uwansa Suleiman ta hanyar sadaukar masa da kodar.

Dama dai Kungiyar Likitocin Cututtukan da suka shafi Kodar na Kasa da Kasa sun sha jaddada cewar a bisa yadda cutar kodar ke ci gaba da hallaka jama'a da dama a kasashen duniya akwai bukatar gwamnatocin kasashe musamman masu tasowa su yi tsayuwar daka wajen samun wadatattun kayan aiki da magunguna a manyan asibitoci domin ceton rayukan al'umma