Kawancen jam'iyyu zai tsayar da dan takara daya don kayar da PDP a Najeriya

Image caption Shugaban hukumar zaben Najeriya ya ce zai gudanar da sahihin zabe

A Najeriya wasu jam'iyyun adawa a kasar goma sha daya sun sanya hannu a kan wata yarjejeniyar kulla wani kawance a wani mataki da suka ce na yi wa jam'iyyar PDP mai mulki, taron dangi ne, domin kayar da ita, a zabukan dake tafe.

Kawancen jam'iyyun dai sun ce, sun amince za su tsayar da dan takara guda, a kowanne zabe, wanda kuma za su mara wa baya ga baki dayansu, tun daga matakin shugaban karamar hukuma har zuwa mukamin shugaban kasa.

Kawancen jam'iyyun mai suna kawancen samar da sabuwar Najeriya wato Coalation for New Nigeria CNN a turance, ya ce a wannan karon ya kudiri aniyar ganin ya cimma burinsa, sabanin abin da ya faru a zaben da ya gabata na kasa hadin kan 'yan adawa.

Jam'iyyun sun kuma bada tabbacin cewa, suna nan suna bin diddigi domin tantance sahihan 'yan takarar da za su tsayar zabe domin mara musu baya.

Kawancen jam'iyyun dai sun hadar da CPC ta Janar Muhammadu Buhari, da PRP ta Alhaji Balarabe Musa, da Labour Party da sauransu.