Martanin Majalisar Najeriya ga hukumar zabe

Shugaban Hukumar Zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega
Image caption Hukumar Zaben ta Najeriya ta ce da ma can kudin da take nema wani bangare ne na kasafin kudinta da aka rage

Majalisar Dokokin Najeriya ta ce sai ta ga wasika daga bangaren zartarwar kasar sannan za ta san matakin da za ta dauka dangane da bukatar Hukumar Zabe ta kasar ta baya-bayan nan.

Dan Majalisar Wakilai Labaran Yunusa Dambatta ya shaidawa BBC cewa: “Mu ba za mu ce wani abu ba a kai, illa namu shi ne [yin] doka; idan aka kawo muka duba [muka ga] cewa ya cancanta a yi doka, shi ke nan”.

Shugaban Hukumar Zaben, Farfesa Attahiru Jega, ya ce hukumar na bukatar kudi naira biliyan takwas, wadanda hukumar ta ce an cire daga kasafin kudinta, domin gudanar da wasu ayyuka da suka shafi zaben kasar wanda za a gudanar a badi.

Mataimakin shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Nick Dazang, ya bayyana cewa hukumar ba ta da ofis-ofis a wadansi jihohi da kananan hukumomi: “To muna so ne a gina wadannan ofis-ofis, kuma a sayi kujeru, a sayi kayan aiki; shi ya sa ake so a koma a samu gwamnati a yi musu bayanin cewa in ba a bayar da wannan kudin ba, to lallai za a samu matsala”.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin Najeriyar ta amince a baiwa hukumar sama da Naira biliyan tamanin domin rajistar masu zabe, adadin da wasu suka rika sukar cewa yayi wa hukumar yawa.

A halin da ake ciki kuma, yayin da zabukan 2011 ke gabatowa a Najeriyar, wani batu da ake muhawara a kai shi ne ko hukumar zaben kasar za ta iya gudanar da zabubbukan a cikin watan Janairun badi ko kuwa a'a.

Yayin da wasu ke ganin hukumar zaben ta shirya kuma tana da karfin gudanar da zabukan a cikin watan na janairun badi, wasu kuwa gani su ke dole sai hukumar ta kara damara tare da sauran masu ruwa da tsaki, muddin Najeriyar na son gudanar da zaben.

A halin yanzu dai hukumar ta INEC ba ta yi rajistar masu jefa kuri'a ba kuma kimanin watanni hudu suka rage zuwa lokacin da ake sa ran hukumar za ta gudanar da zabukan.