Najeriya za ta fuskanci matsalar matasa - In ji British Council

Wani rahoto da hukumar raya al'adu ta Birtaniya wato British Council ta fitar, ya yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar babbar matsalar yawan jamaa, muddin ba ta inganta tattalin arzikinta, tare da samarwa yan kasar dake karuwa a kullum, aikin yi ba.

Rahoton ya ce rashin aikin yi shi ne babban kalubalen da matasa ke fuskanta yanzu haka a kasar.

Haka kuma rahoton yayi kiyasin cewa yawan alummar Najeriya wanda a yanzu ya kai million 150, zai karu da mutane million 63 kafin shekara ta 2050, wanda zai sanya ta, ta zamanto kasa ta ukku a duniya da tafi yawan alumma.

British Council ta ce kafin wannan lokaci, kashi 40 bisa 100 na alummar kasar za su kasance yan kasa da shekaru 14 a duniya.