Obama ya yi Allah wadai da Hamas

Image caption Shugaba Obama da shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas

A ranar da ake bude babin sabuwar tattanawar zaman lafiyar gabas ta Tsakiya, shugaba Obama ya yi Allah wadai da kisan yahudawa hudu 'yan kama wuri zauna da ake zargin mayakan kungiyar Hamas ne suka aiwatar a gabar Yammacin kogin Jordan.

A lokacinda yake ganawa tare da Pira Ministan Israela Benjamin Netanyahu a fadar White House, shugaba Obama ya yi wa Hamas hannun-ka-mai-sanda kai tsaye, inda ya ce irin wadannan hare hare ba za su yiwa yunkurin samar da zaman lafiya katsalandan ba.

Ya ce "sako ga Hamas da duk wanda ke da alhakin aikata wannan laifi, wannan ba zai dakatar da yunkurinmu na tabbatar da tsaron Israela ba, kuma ba zai hana mu kokarin tabbatar da tsaro mai dorewa ba, inda alummar yankin, kowa zai bada gudunmuwarsa."

Tun da farko dai mahukunta a Palasdinu sun kaddamar da daya daga cikin aikin tsaro mafi girma a kan abokan adawarsu na Hamas, bayan da mayakan Hamas din suka halaka Yahudawa 'yan kama wuri zauna guda hudu a gabar yammacin kogin Jordan.

Ministan tsaron Isra'ila Ehud Barak yayi kira da a kai zuciya nesa.

Ya ce "ina fata za mu iya dakatar da irin wannan sabon nau'i na hare haren ta'addanci wanda aka yi domin gurgunta tattaunawar sasantawar da ake farawa yau a Washington".