Obama ya kawo karshen yakin Iraki

Shugaba Obama na Amurka
Image caption Shugaba Obama na Amurka yana gabatar da jawabin da ya sanar da kawo karshen yakin iraki

Shugaba Obama na Amurka ya bayar da sanarwar kawo karshen yakin da Amurka ta fafata a Iraki.

A wani jawabi da ya yi daga ofishinsa na Oval Office (wannan ne jawabi na biyu da Shugaban na Amurka ya yi daga ofishin tun bayan hawansa mulki), wanda kuma aka yada kai tsaye ta gidajen talabijin, Shugaba Obama ya ce Amurka ta sauke alhakin da ya rataya a wuyanta a Iraki, kuma lokaci ya yi da za ta mayar da hanakali wajen farfado da tattalin arzikinta.

“Ina ba da sanarwar cewa yakin da Amurka ta fafata a Iraki ya zo karshe.

“Yakin 'yanto kasar Iraki ya kare, yanzu 'yan Iraki ne ke da alhakin tabbatar da tsaro a kasarsu”, inji Shugaba Obama.

Shugaban na Amurka ya kuma ce ya jinjinawa sadaukar da kan da sojojin Amurka maza da mata suka yi a kasar ta Iraki.

A cewarsa, lokaci ya yi da Amurka za ta bude sabon babi.

Da ya ke magana a kan wanda ya gada, wanda kuma shi ne ya kaddamar da yakin, Shugaba Obama cewa ya yi babu wanda zai yi shakkar kaunar da George Bush ke yiwa kasarsa da kuma damuwarsa da tsaronta.

To amma, a cewarsa, ba rayukan mutanenta kawai yakin na Iraki ya lamushewa Amurka ba:

“Wajibi ne karfin fada-a-jin da muke da shi a waje ya kafu a bisa bunkasar tattalin arzikinmu.

“Babban alhakin da ya rataya a wuyanmu shi ne farfado da tattalin arzikin namu da kuma samar da ayyukan yi ga miliyoyin Amurkawan da suka rasa ayyukansu”.

A cewar Mista Obama, Amurka ta kashe fiye da dala tiriliyan daya a kan yake-yake, akasarinsu kuma bashi ta ciyo daga waje.

To amma wannan ba ya nufin Amurka ta kawo karshen zaman dakarunta a Iraki kwata-kwata ba ne—sojoji dubu hamsin za su ci gaba da zama a kasar don ba da shawarwari da kuma shiga fagen daga in ta kama.

Sai dai shugaban na Amurka ya jaddada alkawarin da ya yi na janye daukacin sojojin Amurka daga Iraki nan da karshen shekara mai zuwa.

Karin bayani