Hamas ta ce za ta cigaba da kai hari kan Isra'ila

Mayakan Hamas
Image caption Mayakan Hamas

Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta yi gargadin cewa zata ci gaba da kai hare hare kan Yahudawa a duk inda suke a yankin Gabar yammacin Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye.

Hamas ta ce ita ce ta kai hari, inda ta bude wuta, tare da raunata wasu 'yan Isra'ila biyu, yayinda shugabanin Palasdinawa da na Isra'ila ke ganawa a Washington domin fara shawarwarin zaman lafiya na gaba da gaba a karon farko cikin kusan shekaru biyu.

Kungiyar Hamas wadda ba a gayyata wurin taron ba, ta ce Jagoran Palasdinawa Mahmoud Abbas ba shi da izinin tattaunawa da yawun Palasdinawa. Ko a ranar Talata, 'yan bindigar kungiyar Hamas sun kashe wasu Yahudawa 'yan kama wuri zauna a gabar Yammacin Kogin Jordan.