Tattaunawa mai armashi tsakanin Isra'ila da Falasdinawa

Shawarwarin zaman lafiya a gabas ta tsakiya
Image caption Shawarwarin zaman lafiya a gabas ta tsakiya

Isra'ila da Falasdinawa sun gudanar da shawarwarin gaba da gaba a karon farko cikin kusan shekaru biyu, a birnin Washington.

Wakilin Amurka na musamman a yankin gabas ta tsakiya, Sanata George Mitchell, ya ce ya zuwa yanzu tattaunawar na yin armashi.

Ya ce bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar sake ganawa da juna, a ranakun sha hudu da sha biyar na wannan watan Satumba, a yankin gabas ta tsakiya, sannan kuma su kara wata ganawar kusan makwanni biyu bayan hakan.