Agaji ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Nijar

Wasu da ambaliyar ruwa ta shafa a Nijar
Image caption Wasu da ambaliyar ruwa ta shafa a Nijar

A jamhuriyar Nijar wata kungiya mai suna Ummah Welfare Trust ta kasar Pakistan ta fara rarraba ma jama'ar da ambaliyar ruwa ta rutsa da su wasu kayayyakin abinci sama da tan 400.

Gwamnan jahar Yamai ne Kanal Sumana Djibo ya kaddamar da shirin a unguwar Lamorde ,daya daga cikin unguwannin Yamai da ambaliya ta yi wa barna. Gwamnan ya ce suna gudanar da shirin ne cikin kyakkyawan tsari saboda haka duk wanda aka yi ma rejista zai samu taimakon da ya hada da kayan abinci da magunguna da gidajen sauron da aka fesa ma magani.

Hukumomin agaji na majalisar dinkin duniya dai sun kiyasta cewa mutane dubu 17 ne ambaliyar ruwan ta rutsa da su a cikin birnin Yamai kadai.