Shugaban Niger ya kori wasu jami'an wani kwamitin bincike

Janar Salou Djibo
Image caption Janar Salou Djibo

Shugaban mulkin sojan Niger, Janar Salou Djibo, ya kori wasu wakilai ukku na kwamitin bincike domin kwato dukiyar kasa.

An ce an kore su ne kan zargin yin sakaci da aikinsu, da kuma aikata wasu abubuwan da suka saba wa ka'idojin aikin kwamitin.

Shugaban ya ce mutanen na kaurace wa wuraren aikinsu har tsawon kwanaki da dama, ba tare da wasu hujjoji ba. Wannan kora ta biyo bayan wata wasikar jan kunne da gargadi da Janar Salou Djibo ya aike wa shugaban kwamitin, Malam Abdoulkarim Mossi a makon jiya, inda yake kokawa a kan halayyar da wasu daga cikin wakilan kwamitin ke nunawa.