Hauhawar farashin kayan abinci na damun kasashe

Jacques Diouf, shugaban hukumar FAO
Image caption Jacques Diouf, shugaban hukumar FAO

Hukumar abinci da bunkasa ayyukan gona ta Majalisar Dinkin Duniya, FAO, ta kira wani taro na musamman domin tattauna farashin kayan abinci a duniya.

Hukumar ta ce ta kira taron ne, wanda za a yi nan gaba a cikin wannan watan, saboda damuwar da kasashe suka nuna akan batun.

Farashin kayan abinci, musamman ma alkama ya yi tashin gwabron zabo, sakamakon matsalar farin da aka fuskanta a wasu sassa na tsohuwar Tarayyar Soviet, da kuma takaita fitar da alkamar da Rasha ta yi.

A kwanakin baya tashin farashin kayayakin abincin ya janyo tarzoma a Mozambique, kuma jama'a sun fusata a kasashe dayawa.