An kashe fataken kwayoyi a Mexico

Sojojin Mexico
Image caption Sojojin Mexico da makaman da suka kwace

Hukumomin kasar Mexico sun bayyana cewa akalla dillalan miyagun kwayoyi ashirin da biyar ne aka kashe a wata musayar wuta da sojoji a arewacin kasar.

Wani mai magana da yawun rundunar sojin kasar ya shaidawa BBC cewa al'amarin ya auku ne a kusa da birnin Ciudad Mier da ke kusa da kan iyakar kasar da Amurka.

Hukumomin na Mexico sun ce sun gano maboyar dillalan miyagun kwayoyin ne yayin wani sintiri na jiragen sama a yankin da ke kan iyakar jihohin Tamaulipas da Nuevo Leon.

Lokacin da sojoji suka tunkari yankin sun fuskanci aman wuta, al'amarin da ya kai ga ba-ta-kashin.

Wannan yanki na kasar dai na fama da karuwar tashe-tashen hankula masu alaka da kungiyoyin dillalan miyagun kwayoyi.

A watan da ya gabata ma an gano gawarwakin wasu bakin haure su saba’in da biyu wadanda ake zargin dillalan miyagun kwayoyi da kashe su bayan sun karbe 'yan kudadensu.

Tashe-tashen hankula irin wadannan dai na kara yaduwa a kasar, yayinda abokan adawar Shugaba Felipe Calderon ke suka a kan matakan sojin da ya ke dauka a kan dillalan miyagun kwayoyi.

Sai dai a wani jawabi da ya yiwa al'ummar kasar, Shugaba Calderon ya kare manufofinsa, yana mai cewa masu aikata laifuffuka abokan gaban daukacin al'ummar kasar ne.

Fiye da mutane dubu ashirin da takwas ne dai suka rasa rayukansu sakamakon tashe-tashen hankulan da suka jibinci miyagun kwayoyi a Mexico tun shekarar 2006.