An baza jamian tsaro a kasar Mozambique

Masu zanga-zanga a Mozambique
Image caption Zanga-zangar Mozambique

An baza dimbin jami'an tsaro a wasu sassan Moputo, babban birnin kasar Mozambique, sakamakon kwanaki biyu da aka shafe ana tashin hankali kan tsadar farashin kayayyakin abinci da ya yi sanadiyar mutuwar mutane bakwai tare da raunata kusan dari uku.

Rahotanni sun ce 'yan sanda ne suka bude wuta a kan masu zanga-zanga.

Wakilin BBC dake Moputon ya ce al'amura sun fara lafawa, sai dai har yanzu makarantu da shaguna da dama na ci gaba da kasancewa a rufe.

Zanga zangar ta samo asali ne sakamakon karin farashin buredi da aka yi da kaso talatin cikin dari, kuma gwamnati ta ce ba za a soke karin farashin ba.