CSRD ta gyara sabon tsarin mulkin Nijar

Shugaban Majalisar Mulkin Sojan Nijar Salou Djibo
Image caption Shugaban gwamnatin sojan Nijar, Salou Djibo

A daren jiya, Majalisar Mulkin Soja ta Jamhuriyar Nijar, CSRD, ta ce ta yi gyaran fuska ga sabon kundin tsarin mulkin da majalisar tuntubar juna ta gabatar mata a makon jiya.

Daga cikin sauye-sauyen da sojojin suka yi har da soke ayar dokar da ta tilastawa ’yan takarar shugabancin kasar kammala karatun jami'a da kuma takaita shekarunsu zuwa kasa da saba'in a duniya.

Kakakin Majalisar Mulkin Sojan, Kanar Goukoye Abdoul Karim, ya shidawa BBC cewa sun yi hakan ne saboda, “yau idan aka duba [a] wadansu kasashe ana samun mutane wadanda ba wani babban ilimi ba aggaresu, amma da yake mutane ne masu kishin kasa—kuma ka san dama aka ce babu mugun sarki sai dai mugun bafade.

“To idan wannan mutumin ya samu fada ta kwarai—ya samu mutanen da za su taimaka mai—kuma shi yana da kunnen ji, muna lissafi in dai mutum ne mai kishin kasa, zai ja kasan nan yadda ya kamata”.

Kakakin ya kuma ce a sabon tsarin da majalisar da shirya mai shekaru talatin da biyar ka iya shiga takarar zama shugaban kasa.

Dangane da ‘yan majalisar dokoki kuwa, wadanda aka bukaci su kasance masu ilimi mai zurfi, Kanar Abdoul Karim cewa ya yi ya kamata kashi uku cikin hudu na ‘yan majalisar su kasance masu ilimi, sauran rubu’in kuma, ko ba su da ilimi mai zurfi ya kasance jama’ar da suke wakilta sun gamsu da su.

“Abin da nake so a gane”, inji shi, “[shi ne:] aikin majalisa aiki ne wanda sai da ilimi”.

Wannan matakin da sojojin suka dauka zai taimaka wajen dakushe kaifin zargin da wasu 'yan kasar ke yi cewa sojojin na nuna wariya ga wasu 'yan kasar.

A watan Maris mai zuwa ne dai sojojin suka yi alkawarin rantsar da sabon zababben shugaban kasa.