An sami manyan mutane da laifin lalata da yara a Portugal

Cin zarafin yara a Portugal
Image caption Cin zarafin yara a Portugal

Wata kotu a kasar Portugal ta samu dukan mutane 7 din da ake zargi da cin zarafin yara a wani gidan marayu na kasar da laifi.

An dauki shekaru da dama ana gudanar da wannan shari'a.

Wadanda aka samu da laifin sun hada da daya daga cikin masu gabatar da shirye-shiryen talabijin din da suka fi shahara a kasar, Carlos Cruz, da kuma wani babban jami'in diplomasiya.

Carlos Cruz ya ce hukuncin wani kuskure ne na shari'a a tarihin kasar Portugal, kuma tamkar daukar fansa ne a kan shi.