Za a yi zanga zanga a Faransa

Shugaban kasar Faransa, Nicholas Sarkozy
Image caption Za a gudanar da zanga zanga a Faransa

A kasar Faransa, yau ne ake saran fara wata zanga zangar nuna adawa da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na maida 'yan Roma kasashen su.

Kungiyoyin dake fafutikar yaki da nuna wariyar launin fata da sauran kungiyoyi dake adawa da matakin da gwamnatin ta dauka, na saran, fiye da mutane dubu talatin ne zasu shiga cikin zanga zangan a birnin Paris kadai.

Matakin yayi sanidiyar maida kusan 'yan Roma mutum dubu daya zuwa kasarsu da kuma Bulgaria a watan da ya gabata.

Kasashen duniya da dama sun yi ta sukar matakin da gwamnatin Faransa ta dauka.

Sai dai a bangare daya kuma, jama'a da dama a kasar sun yi marhabin da matakin na gwamnati.

Binciken jin ra'ayoyin jama'a ya nuna cewa, kusan kashi sittin na jama'ar kasar sun yi ammanar cewa matakin da gwamnatin ta dauka yaya dai dai.