Hukumomin Saudiyya sun sako Sheikh Ahmad Gumi

'Yan sanda a Saudiyya
Image caption 'Yan sanda a Saudiyya

Hukumomin kasar Saudiyya sun sakko Sheikh Ahmad Gumi bayan tsarewar da suka yi masa tun watan Fabrairun wannan shekarar.

An sakko Sheikh Ahmad Gumi din ne ba tare da wata tuhuma ba. A wata hira da yayi da BBC bayan an sako shin, Sheikh Ahmad Gumi ya ce kamashin da hukumomin Saudiyya suka yi yana da alaka da mahunkuntan Nijeriya.

A cewarsa a shekara ta 2007, gwamnatin tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ta aika wani sako kan harkokin tsaro ga gwamnatin Saudiyya domin yin batanci a gareshi, amma bayan yunkurin da dan Nijeriyar nan Umar Farouk Abdulmutallab yayi na tarwatsa jirgin Amruka a watan Disamba na bara, sai hukumomin Saudiyya suka fara gudanar da bincike akansa.

A lokacin da suke binciken ne suka ga wayar mahaifin Umar Farouk da kuma shi kansa Umar Farouk din a wayar salularsa, dalilin da ya sa jami'an Saudiyyar suka ce zasu gudanar da dogon bincike.

Sheikh Ahmad Gumi ya ce an sallame ba tare da tuhuma ko gindaya sharadi ba.