Hukumar zabe ta yi kuskure, inji Nyako

Shugaban hukumar zabe,Farfesa Attahiru Jega
Image caption Gwamna Nyako ya ce hukumar zabe ta yi kuskure

A Najeriya,gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako ya ce hukumar zabe mai zaman kanta, ta yi kurkure dangane da batun nan na yin sabon zabe badi a jihohi shida inda a baya aka soke zabensu.

Gwamnan ya shaidawa BBC cewa, kudirin hukumar ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, wanda ya ce duk zaben da aka soke,sannan aka gudanar da wani daidai yake da gudanar da sabon zabe.

Ya ce, : ''A cikin kudin tsarin hukumar zaben an ce, ranar da aka gudanar da wani sabon zabe,wato ranar da aka rantsar da wanda ya lashe shi, ita ce ranar da za a fara kidaya wa'adin da mutum zai yi.Hakan na rubuce(a kundin tsarin mulki).Don haka ko a zamanin soja ba zamu yi doka sannan a ce ta fara aiki a shekarun da suka wuce ba."

Gwamna Nyako ya yi kira ga shugaban hukumar zaben ya hukunta duk mutumin da ke da alhakin abinda ya kira, karya doka,ta hanyar bada shawara kan sauke abinda kotun koli ta yanke hukunci a kai.

Ita dai hukumar zabe tace ta dauki wannan mataki ne bisa biyayya ga doka