Fargabar ambaliya a Sakkwato: Kogin Goronyo na malala

Jama'a na fargabar barkewar ambaliya saboda malalar ruwa a kogin Goronyo, a daidai lokacin da daruruwan iyalai daga wani kauye da ambaliyar ruwa ta hadiye a yankin karamar hukumar Goronyo ta jihar Sakkwato suka shiga kwana na hudu a sansanonin 'yan gudun hijira.

Sauran alu'mmomin da ke makwabataka da su na fuskatar barazanar fadawa cikin irin wannan halin sakamako fara malalowar ruwa daga madatsar ruwa ta goronyo zuwa cikinsu.

Rahotanni daga yankin sunce dimbin mazaunansa ne yanzu ke can suna yaki da ruwa dake kokarin ketarowa zuwa cikin kauyukansu bayan da madatsar ruwa ta cika ta batse.