Dangote ya aika da gagarumin taimakon kayan abinci Nijer

Hamshakin dan kasuwar nan na Nijeriya, Alhaji Aliko Dangote ya aika da taimakon kayan abinci da aka yi kiyasin zasu kai na Naira miliyan dari, ko CFA miliyan dari uku da 'yan kai, zuwa Jamhuriyar Niger.

Kamar yadda mataimakin jakadan Nijeriyar a Nijer, Alhaji Muhammadu Sani Yunusa ya shaidawa wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou, taimakon ya biyo bayan kiran da hukumomin Niger ke cigaba da yi ne, na a agazawa kasar sakamakon karancin abinci da ambaliyar ruwan da take fuskanta.

Tun farko dai an ga motocin na Alhaji Aliko Dangote a kan iyaka da jamhuriyar Nijer, abinda ya saka fargaba a zukatan wasu 'yan Niger ko an sami matsala ne kan harkokin shige da fice, batun da mataimakain jakadan Nijeriya yai karin haske akai.