Sabbin zarge-zarge kan 'yan wasan Kurket na Pakistan

Rao Iftikahar,dan wasan kurtet ne a pakistan
Image caption Jaridar Burtaniya ta yi sabbin zarge-zarge kan 'yan wasan Pakistan

Wata Jarida a Burtaniya maisuna The News of the World a turance, ta buga wasu sabbin zarge-zarge da take yiwa 'yan wasan Kurket na kasar Pakistan.

Editan sashen wasannin na jaridar, Paul McCarthy ya shaidawa BBC cewa, akwai zarge-zarge guda ashirin da uku da ake yiwa 'yan wasan su uku.

Ya ce:''A duk zargi guda daya mun buga kimanin shafi shida.Kuma muna iya cewa hukumar dake sa ido akan wasan kurket din ta duniya, ta gargadi kaftin din kungiyar maisuna Salman Butt har sau biyar, kan nauyin dake kansa, da ya shafi kai rahoton duk wata ganawa da suka yi da wadanda ba 'yan kasar ba ne.Mun sani cewa hukumar na binciken mutum na hudu akan batun''.

'Ya yi watsi da batun jakadan Pakistan'

Mista McCarthy ya yi watsi da zargin da jakadan Pakistan na kasar Ingila,Wajid Shamsul Hassan ya yi cewa,shaidun nasu na jabu ne.

Ya ce:''Muna wallafa shafi goma sha takwas ne kan batun na kwallon kurket, kuma shafuka takwas na magana ne dungurungum kan abubuwan da suka wakana game da wannan badakala;kama daga sakonnin kanta kwanan da 'yan wasan suka aikewa da junansu.Don haka batun da jakadan ke yi ba gaskiya ba ne.Hasali ma hakan zai sa a rika yi masa kallon biyu ahu''.

Wadannan zarge-zarge sun zo ne mako guda tun bayan da jaridar ta fallasa batun badakar da ta shafi 'yan kwallon kurket din na Pakistan.