'Adamawa na kokarin maganin amai da gudawa'

Daya daga cikin mutanen dake fama da cutar amai da gudawa a Najeriya
Image caption Gwamnatin Adamawa ta ce tana kokarin magance cutar

A Najeriya, gwamnatin jihar Adamawa ta ce tana daukar matakan shawo kan cutar amai da gudawa da ta barke a wasu sassan jihar,wacce rahotanni suka ce ta hallaka mutane da dama.

Gwamnatin jihar ta ce, yanzu haka tana gudanar da wani shirin samar da ruwan sha mai tsabta ga jama'ar jihar.

Gwamnan jihar Adamawan, Murtala Nyako ya shaidawa BBC cewa, suna hada gwiwa da gwamnatin tarayya don samar da magungunan cutar amai da gudawar.

Hukumomin lafiya na kasar, sun ce mutane kusan dari uku da hamsin ne ya zuwa yanzu cutar ta amai da gudawa ta hallaka.