An jingine yajin aiki a Afrika ta Kudu

ma'aikata a Afrika ta Kudu
Image caption Ma'aikatan Afrika ta Kudu sun jingine yajin aiki.

A Afrika ta Kudu, an jingine yajin aikin da ma'aikatan gwamnati su sama da miliyan guda suke gudanarwa. Shugabannin kungiyoyin kwadago sun ce ba sun amince da tayin da gwamnati ta yi masu ba ne, amma zasu dakatar da yajin aikin na tsawon makonni uku, domin baiwa 'ya'yan kungiyar damar nazari kan tayin gwamnatin.

Masu lura da al'amurra sun ce yajin aikin, wanda ya haddasa rufe asibitoci,da makarantu ya janyo tsamin dangantakar siyasa tsakanin gwamnatin Afrika ta Kudu, da kungiyoyin kwadago.

Ana kiyasin cewa kasar tana asarar dala miliyan dari da arba'in a kowace rana, sakamakon yajin aikin.