Mutane 36 sun mutu a Guatemala

Wadansu masu aiki ceto a kasar Guetemala
Image caption Hukumomi sun ce mutane talatin da shida ne suka mutu

Hukumomi a kasar Guatemala, sun ce akalla mutane talatin da shida ne suka mutu, sanadiyar zaftarewar kasa,wacce ruwan sama kamar da bakin kawarya,wanda aka kwashe makonnin ana yi kasar ya jawo.

Tsaunuka sun ruguje kan dandazon mutanen da suka taru, don fitar da wata motar bas,wacce ta makale akan wani titi dake arewa da babban birnin Guatemala.

An gano akalla gawawwaki ashirin,sai dai masu aikin ceto sun dakatar da neman da suke yiwa kimanin mutane arba'in,wadanda suka bace.

Sun ce sun yi hakan ne saboda fargabar ci gaban aukuwar zaftarewar kasar.

Mario Guzman Soto,wani ma'aikacin kwana-kwana ne, wanda ke taimakawa wajen gudanar da aikin ceton, kuma ya shaidawa manema labarai cewa aikin na jan kafa.

Wani mazaunin yankin masuna Efrain Ocoto,ya ce aikin neman wadanda suka tsira daga zaftarwar kasar zai ci gaba.

Ya ce:''A yanzu masu aikin kwana-kwana sun shaida mana cewa har yanzu akwai mutanen da basu iya cetowa ba.Muna fatan zasu iya ceto su,abinda zai sa mu mika su ga iyalansu''.