Jamus zata ci gaba da amfani da tashoshin nukiliya

Wata tashar nukiliya a kasar Jamus
Image caption Jamus zata ci gaba da amfani da tashoshin nukilyarta

Wani babban taro da ake gudanarwa a birnin Berlin na kasar Jamus, ya amince kasar ta ci gaba da amfani da tashoshin nukiliyarta.

Taron wanda ya kunshi 'yan siyasa da masu masana'antu,ya ce yin amfani da tashoshin na samar da wutar lantarki cikin sauki.

Sai dai masu adawa da batun sun ce hakan nada hadari,domin babu wata hanya da za a iya kawar da gurbatacciyar iskar da tashoshin ke fitarwa.

Yin amfani da tashoshin nukiliya don samar da wutar lantarki batu ne mai sarkakiya a kasashe da dama.