'Yan sanda na bincike kan kisan boye a Maiduguri

Marigayi Muhammad Yusuf, shugaban Boko Haram
Image caption Marigayi Muhammad Yusuf, shugaban Boko Haram

'Yan sanda a arewa maso gabashin Nijeria na gudanar da bincike dangane da wasu jerin kashe-kashe, wadanda suke fargabar cewa, alamun sake farfadowar kungiyar nan ce ta Boko Haram.

Mutane fiye da goma ne, ciki har da 'yan sanda da mahukunta a yankin aka halaka, cikin watanni biyun da suka gabata a birnin Maiduguri dake jihar Borno.

Mutanen da wannan hari ya rutsa da su dai har da Lawanin unguwa , Lawan Zanna Mohammed Kagu wanda lamarin ya faru a kofar gidansa lokacin da suke shirin fara sallar isha'i.

Kimanin watanni biyu kenan da yan bindigar suka fara aiwatar da kashe-kashen 'yan sanda da masu unguwanni, lamarin da yanzu haka ke dada jefa zullumi da fargaba a cikin zukatan jama'a.

Rundunar 'Yansanda ta jihar Bornon ta ce, tana nan tana gudanar da bincike kan lamarin.