Wani dan kunar bakin wake ya tayar da bom a Pakistan

Wani dan kunar bakin wake ya kutsa cikin wani caji ofis da wata mota makare da bama-baman da ya tarwatsa ginin da ofishin 'yan sandan suke, a arewa maso yammacin Pakistan.

Tashin bam din da ya auku ne a birnin Lakki Marwat, dake yankin Kyber wanda yayi sanadiyyar rasuwar mutane 19, ciki har da 'yan sanda guda tara da yara kanana da dama.

Wannan ne harin kunar bakin wake na ukku da aka kai a Pakistan cikin yan kwanakin baya bayan nan.