Afrika ta kudu ta kara albashin ma'aikata domin dakatar da yajin aiki

Sama da ma'aikata miliyan daya ne suka shiga yajin aikin
Image caption Sama da ma'aikata miliyan daya ne suka shiga yajin aikin

Gwamnatin kasar Afrika ta kudu ta kara albashin sama da ma'aikta miliyan guda da suka yi yajin aiki.

Shugaban kasar Jacob Zuma ya nemi da a kara zama a teburin sulhu ne ganin cewa yajin aikin ya dauki tsawon makwanni biyu, abinda ya kaiga rufe makarantu da dama da kuma asibitoci.

A lokacin wata doguwar tattaunawa sa wakilan gwamnati da na kungiyoyin kwadago wakilan gwmnati sun yi tayin karin kashi bakwai da rabi cikin dari na albashi ma'aikatan, yayinda kungiyoyin kwadago suka nemi ayi mu su karin kashi takwas digo shida.

Kungiyoyin dai a karshe sun yanke shawarar kada kuri'a game da tayin karin gwamnati.

Tsugune bata kare ba

Zwelenzima Vavi, sakatare janar na kungiyar 'yan kasuwa mafi girma a kasar ya shaidawa BBC cewar kungiyarsa na kokarin ganin ta tilatta wa gwamnati yin karin kashi takwas din.

"Mun tattauna da gwamnati sosai, kuma mun nuna babu gudu ba ja da baya, amma ina ganin nan da mako guda zuwa biyu, gwamnati za ta amince da bukatun mu."

"Yanzu dai batun ya rage ga ma'aikata, ko za su iya ci gaba da yajin aiki, ko kuma za su amince da tayin gwamnati."

Yajin aiki dai ya sanya ayyuka a asibitoci kusan sun tsaya cik, lamarin da ya kaiga sojoji likitoci da 'yan sa kai ke kulawa da mutane.

Wajen kima ma'aikata dubu daya ne suka shiga yajin aiki a kasar, kuma masana na ganin cewar muddin kungiyar 'yan kasuwa suka shiga yajin aiki, yawan masu yajin aikin zai ninka.

Image caption Mista Zuma na neman sulhu ne domin cimma manufofin siyasa

Wakiliyar BBC ta ce Mista Zuma yana neman sulhu ne da masu yajin aikin saboda ya kare martabarsa ta fuskar siyasa.

Masu yajin aikin sun soki Mista Zuma saboda ziyarar ran gadi da ya kai China, a yayinda ake ci gaba da yajin aiki a kasar.

Shugaban kasar dai na so ya gyara dangantakarsa da kungiyoyin kwadago a kasar wadanda ake ganin suna ba shi mahimmin goyon baya a harkar siyasa, kafin babban taron jam'iyyar sa ta ANC anda zai tattauna a kan manufofin gwamnati.