Teloli na cacar baki da masu kaya

Yadunan sayarwa a kasuwar kantin Kwari dake Najeriya
Image caption Teloli da masu kai dinki na cacar baki

A Najeriya, a lokacin da bikin sallah karama ke gabatowa,teloli da kuma wadanda kan kai musu dinki, sun fara cacar baki kan rashin cika alkawuran telolin.

Wadansu da suka kaiwa telolin dinki sun shaidawa BBC cewa, yawancin telolin na yin zari wajen karbar dinkin,abinda ke sa su rashin baiwa wadanda suka kai dinkin kayansu akan lokaci.

Jamilu Baba Dara-Dara,na daga cikin mutanen da suka kai dinkin sallar tun kafin watan azumi ya kama,amma ya ce telansa ya karya alkawari wajen ba shi kayan nasa.

Sai dai a nasu bangaren,telolin sun dora laifin ga masu kayan,inda suka ce wasunsu na takurawa akan dole sai an dinka musu kayan,koda kuwa basu kai dinkin akan lokaci ba.