Jam'iyyar ANPP ta nada shugabannin riko

Taswirar Najeriya
Image caption Jam'iyyar ANPP ta nada shugabannin kwamatin riko

A Najeriya, babbar jam`iyyar adawa, ANPP ta kaddamar da kwamitin rikon shugabancinta na kasar sakamakon cikar wa`adin mulkin shugabannin nata.

Jam`iyyar dai ta kaddamar da kwamitin ne a cikin wani yanayi na rudani, kasancewar wasu daga cikin `ya`yanta sun nemi kotu ta dakatar da shugabannin jam`iyyar wajen kafa kwamitin rikon. Shugaban kwamatin rikon,Malam Abdurrahman Adamu ya ce zai kira shugabannin jam'iyyar na sassa daban-daban don tattaunawa kan mafita ga jam'iyyar.

Tun a makon da ya gabata ne dai aka samu baraka a jam`iyyar bayan wani bangaren `ya`yanta ya sanar da sauke shugabannin, saboda a cewarsa wa`adin mulkinsu ya kare tun a ranar biyu ga wannan watan.

Su kuwa shugabannin jam`iyyar sun sanar da korar daya bangaren daga cikin jam`iyyar.