"Yan Boko Haram" sun kai hari a Bauchi

Rahotanni daga Najeriya sunce wasu da ake zargin yan kungiyar addinin Islaman nan ce ta Boko Haram wadda ta tayar da bore a bara, sun kai hari a wani gidan yarin garin Bauchi.

Rahotannin sunce kwamishinan yansanda na Jihar, Alhaji Danlami Yar'adua ya ce mutanen da aka yi amannar yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a kan gidan yarin da yammaci a wani kokari na kubutar da yan uwansu.

Ya ce da isarsu gidan yari suka soma harbi domin samun damar shiga, to amma nan da nan aka tura yansandan kwantar da tarzoma, wadanda suka tinkare su sannan kuma suka shawo kan lamarin.

Wani mashawarcin Gwamnan Bauchin ma ya tabbatar da harin. Dukaninsu kuma sunce an shawo kan lamarin , amma babu daya daga cikinsu da ya ce ko an kashe wani ko kuma wani fursuna ya tsere.

Ba a kuma san ko yan kungiyar nawa ne keda hannu a al'amarin ba.

Harin dai ya zo ne bayan harbe harben kashe mutane a yan kwanakin nan a Jihar Borno ta arewacin kasar, wadanda yansanda ke dora alhakinsu kan yan kungiyar ta Boko Haram.