'Yan bindiga sun farma gidan yarin jahar Bauchi

Taswirar Najeriya
Image caption Wasu 'yan bindiga da har yanzu ba'a san ko su wanene ba sun farma gidan yarin jahar Bauchi inda suka kubutar da wasu fursunoni

Wasu 'yan bindiga da har yanzu ba'a tantance ko su wanene ba sun farma gidan yarin jahar Bauchi dake kusa da fadar mai martaba Sarkin Bauchi.

An dai kone wani bangare na gidan yarin kuma anyi barin wuta tsakanin 'yan bindigar da kuma 'jami'an tsaro.

Sai dai 'yan bindigar sunyi nasarar kubutar da wasu daga cikin fursunonin cikin gidan yarin, kodayake har yanzu ba'a san ko su nawa aka kubutar ba.

Wani babban jam'in gwamnatin jahar Bauchi Alhaji Abdulmuminu Kundak ya tabbatar wa da BBC cewar bincike ne kadai zai tabbatar da ko su wanene suka aikata wannan aiki.

A da dai ana zargin 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne amma sai dai mutanen sun bar wasu wasiku suna masu nisanta kansu da 'ya'yan kungiyar ta Boko Haram

Ana dai fargabar cewar anyi asarar rayuka da kuma jikkata mutane yayin kai wannan hari sai dai har ya zuwa yanzu gwamnatin jahar bata ce ga yawan wadanda suka mutun ba ko kuma suka jikkata