Ana cigaba da aikata fyade a gabacin Congo

Tutar Jamhuriyar damukradiyar Congo
Image caption Majalisar dinkin duniya tace dakarun samar da zaman lafiya a gabacin kasar Congo sun gaza wajen baiwa mata kariya daga yi musu fyade a yankin.

Wani babban jami'in majalisar dinkin duniya ya ce dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya sun gaza wajen kare mata da kananan yaran da ake yiwa fyade a gabashin jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a watan jiya.

Jami'in, Atul Khare ya shaidawa kwamitin tsaron majalisar cewa adadin matan da aka yiwa fyaden zai kai dari biyar.

Jakadiyar majalisar dinkin duniya kan laifuffukan da suka danganci wariyar jinsi, Margot Wallstrom ta shaidawa BBC cewa lokaci ya yi da kasashen duniya za su dau mataki kan lamarin.

Tace ya zama wajibi ga kasashen duniya su hada kai su yi amfani da duk wata dama da suke da ita su baiyana cewa ba za su amince da irin wannan ta'asa ba, kuma za su hukunta masu laifin.