Obama zai inganta abubuwan more rayuwa

Shugaban Amurka,Barack Obama
Image caption Obama ya bayyana shirinsa na inganta abubuwan more rayuwa

Shugaban Amurka, Barack Obama, ya sanar da wani shiri da za'a kashe dala biliyan dubu hamsin wajen samar da abubuwan more rayuwa a kasar .

A wani jawabi da ya yiwa ma'aikata a Milwaukee,Mista Obama ya ce, za'a sake gyara wasu manyan hanyoyi a kasar, kana a inganta hanyoyin sufurin jiragen kasa da kuma filayen jiragen sama.

Ya ce:''Wannan shiri ne da zai samar da riba.Ba zai kara gibin abubuwan more rayuwar kasarmu ba.Don haka zamu hada gwiwa da majalisar dokoki don ganin mun cimma nasara.Za mu kafa wani banki da za a ajiye kudaden da zamu rika samar da abubuwan more rayuwa.Zamu ci gaba da shirinmu na rage cunkoson abubuwan hawa''.

Mista Obama ya soki 'yan jam'iyar adawa ta Republicans,wadanda ya ce suna saka siyasa ga duk wani batu da zai kawo ci gaba ga kasa,madadin su duba kyawunsa.