Akalla mutane 20 sun rasu a harin bam a Pakistan

Harin bam a Pakistan
Image caption Harin bam a Pakistan

Mutane akalla 20 sun hallaka, a lokacin da wani bam ya tashi a hedkwatar 'yan sanda a arewa maso yammacin Pakistan.

'Yan sanda sun ce wasu mutanen masu yawa kuma sun samu raunuka a lokacin tarwatsewar bam din, a garin Kohat.

A jiya Litinin, wani dan kunar bakin wake ya hallaka mutane 19, bayan da ya kutsa da mota makare da bama-bamai a cikin wani ofishin 'yan sanda, a garin Lakki Marwat.

An sami karuwar tashe-tashen hankula sosai a Pakistan a mako gudan da ya wuce.