Masu gudun hijira 'yan Somalia a turai sun sami goyan baya

Wasu 'yan gudun hijirar kasar Somalia
Image caption Masu gudun hijira 'yan kasar Somali a turai sun sami goyan bayan hukumar kula da masu gudun hijira ta majalisar dinkin duniya

Shugaban hukumar kula da masu gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres ya roki kasashen yammacin Turai kar su maida yan gudun hijirar Somalia zuwa kasarsu ta haihuwa.

Mr. Guterres na magana ne a ziyarar da ya kai wani sansani da ke Arewa maso yammacin Kenya inda fiye da yan gudun hijira dubu saba'in mafi yawancinsu 'yan Somalia suke.

A bana dai, kimanin mutane dubu dari biyu ne suka tserewa yake-yaken da ake yi a Somalian.