Mutane 4 sun hallaka a harin gidan kurkukun Bauchi

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 4 tare da jikkatar wasu mutanen kimanin 5, sakamakon farmakin da wani gungun mutane da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne, ya kai a babban gidan yari na garin Bauchi.

Ana dai jin da ma fursunoni kimanin 700 ne a gidan yarin, kuma akasarinsu sun tsere sakamakon samamen.

Amma rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta yi nasarar sake kamo wasu daga cikinsu.

Jiya da almuru ne mutanen suka kai farmaki a gidan kurkukun Bauchin, inda suka yi ta harbe-harbe da bindigogi, tare da cinna wa wurin wuta.

Maharan sun bar wasu takardu wadanda a cikinsu suke cewa, su ba 'yan Boko Haram ba ne.