Kamfanoni na da laifi a malalar mai a tekun Mexico

Kamfanin man BP
Image caption Kamfanin man BP

Kamfanin man BP ya ce akwai laifin kamfanoni da dama a lamarin kwararar man da aka samu a yankin tekun Mexico.

Kamfanin na BP ya bayyana hakan ne, yayinda yake bada bahasi a karon farko, kan bala'in da ya faru a cikin watan Aprilu.

Ma'aikata 11 ne suka mutu, lokacin da rijiyar mai ta yi bindiga, lamarin da ya janyo cikas ga ayyukan kamun kifi da kuma na yawon shakatawa.

Binciken da kampanin na BP ya gudanar na cikin gida ya nuna cewar, abubuwa ne da dama suka hadu suka haddasa aukuwar bala'in.

Kampanin yana fuskantar biyan diyya ta dubban miliyoyin daloli.