Kwalara ta kashe fiye da mutane 700 a Najeriya

Mai fama da cutar kwalara
Image caption Mai fama da cutar kwalara

Ma'aikatar Lafiya ta Najeriya ta bayyana cewa, kawo yanzu mutane 781 ne suka rasa rayukansu daga cikin mutane dubu 13 da suka kamu da cutar amai da gudawa ko kuma kwalara, a kasar.

Ministan lafiya na Najeriyar, Alhaji Sulaiman Bello ne ya bayyana hakan, inda kuma ya kara da cewar a halin yanzu cutar ta fi kamari a jihohin Jigawa da Katsina da Adamawa.

Ministan ya kuma ce ba a tabbatar da bullar cutar a jihohin Osun da Rivers ba, kamar yadda wasu rahotanni su ka nuna.

Tun watan Yunin bana ne dai cutar ta kwalara ta bayyana a wasu sassa na Najeriyar, musamman ma a jihohin arewa.