An fitar da sabon jadawwalin zabe a Nijar

Wata mata na jefa kuria a Nijar
Image caption Zaben dake tafe a Nijar zai maida kasar bisa tafarkin Demokradiyya

A jamhuriyar Nijar hukumar zabe mai cikakken 'yanci, CENI ta tsaida ranar 31 ga watan janairu na shekara mai zuwa a matsayin ranar gudanar da zaben shugaban kasa zagaye na farko da zaben 'yan majalisar dokoki.

Haka nan ta ce za a rantsar da sabon shugaban kasa ran 6 ga watan afrilu maimakon ran 11 ga watan Maris da tun farko aka tsayar.

Hukumar zaben wadda ta bayyana wannan matsayi a yau, lokacin wani taro da wasu 'yan siyasa da sauran manyan jami'ai a shirye shiryen zaben, ta kuma ce tana fuskantar matsaloli wajen rajistan yan Nijar da ke zaune a kasashen waje, lamarin da ta ce zai iya janyo cikas ga zaben a kasashen da suke.