Musulmi sun yi Idi a Nijar

Al'umar musulmi a jamhuriyar Nijar sun yi idin Sallah karama bayan da Ministan cikin gida, Dokta Cisse Ousmane ya bada sanarwa a gidan talabijin na kasar cewa an ga watan Shawwal a jihar Agadez, abinda ya kawo karshen azumin watan Ramadhana a jamhuriyar ta Nijar.

Mutane da yawa da suka zanta da wakilinmu a ranar sun bayyana jin dadinsu da hamdalarsu game da yadda suka yi bukin. Haka nan kuma sun yi fatan Allah ya samar da zaman lafiya da damuna mai albarka a kasar, tare kuma da fatan an gudanar da zaben gaskiya da adalci domin samun Shugaba na gari.

Sai dai a wasu wurare a cikin kasar,wasu mutane ba su yi sallar ba saboda a cewarsu sai sun ga watan da idanunsu.