Obama yayi Allah wadai da barazanar kona Al-Qura'ani mai tsarki

Shugaba Obama
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaba Obama ya yi wani roko na gaggawa ga wani limamin Kirista a Florida, wanda ke shirin kona Al'Kur'ani mai tsarki, da ya dakatar da wannan aniya tasa.

A cikin wata hirar talabijin da aka yi da shi, shugaba Obama ya ce yin hakan, daba ma ciki wuka ne, kuma hanya ce da zata kara baiwa 'yan kungiyar Alka'ida karin magoya baya.

Shugaba Obama ya ce, "idan yana saurare, ina fatan zai fahimci cewa abin da yake shirin yi, ga baki daya ya saba wa dabi'unmu na Amurkawa, wanda ke nuna cewar an gina wannan kasa ce kan harsashin bada 'yancin yin addini, da kuma hakuri da juna".

Hukumomin Amurka dai sun ce tsarin mulkin Amurka ya takaita masu iya matakan da zasu iya dauka kan batun.