An yi ta zanga-zanga kan barazanar kona al Qura'ani mai tsarki

Masu zanga-zanga a Pakistan
Image caption Masu zanga-zanga a Pakistan

Musulmin da suka harzuka sakamakon barazanar da wani fadan Cocin Amurka ya yi na kona kwafe kwafe na al-Qura'ani mai tsarki na ta yin zanga- zanga a sassa daban-daban na duniya.

Paston, Terry Jones ya ce ya dage shirinsa bayan roko daga Gwamnatin Obama.

Barazanar ta sa ta haddasa zanga zanga mai tarzoma a Afghanistan.

Yansanda a can sun ce mutane 3 ne aka harbe, aka kuma raunata a lokacin daya daga cikin zanga zangar a wajen sansanin sojin kungiyar tsaro ta NATO.

A Pakistan masu zanga- zangar sun kona tutar Amurka. Shugaban Indonesia ya yi Allah wadai da shirin kona Al-Qura'anin a matsayin wata barazana ga zaman lafiyar duniya