'Yan Nijar dake zaune a waje ba za su kada kuri'a ba

Wata mai jefa kuri'a a Nijar
Image caption Wata mai jefa kuri'a a Nijar

A jamhuriyar Nijar yan kasar da ke zaune a kasashen waje ba za su jefa kuri'a ba a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Gwamnatin mulkin sojan ta CSRD ce ta dauki wannan mataki sakamakon wani taro karo na biyu da ministan cikin gida Dr Cisse Ousman ya yi da shugabannin hukumar zabe CENI da wakilan jam'iyun siyasan kasar.

A cewar hukumar zaben akwai matsaloli da take fuskanta da suka hada da rashin kyakkyawar rajista da kuma kudin da zaa yi amfani da su wajen shirya zaben.

Sai ra'ayoyin yan siyasar kasar sun sha bamban dangane da wannan mataki da gwamnatin ta dauka, inda wasu ke goyon bayan matakin, wasu kuma ke adawa da shi.