Shugaba Obama ya bukaci karin juriyar addini

Masu zanga-zanga a Pakistan
Image caption Masu zanga-zanga a Pakistan

Shugaba Obama yayi kira ga Amurkawa da su ci gaba da girmama addinanda ba nasu ba, yayinda zanga zanga a

Shugaba Obama yayi kira ga Amurkawa da su ci gaba da girmama addinanda ba nasu ba, yayinda zanga zanga a kasashen musulmi ke ci gaba da karuwa bayan barazanar kona Alqura'ani da shugaban wata karamar mujami'a yayi.

Shugaba Obama ya ce kona littattafan addini ya sabawa duk wasu manufofin da aka kafa kasar Amurka a kansu.

Shugaba Obama ya ce "manufar kona littattafan addinan wasu ta sabawa manufofin kasar nan, ya sabawa abubuwan da aka kafa kasar nan a kai, kuma fata na shi ne mutumin da ya kulla wannan aniya yayi addu'a sannan ya dakatar da aniyar tasa".

Tun farko da ranar dai Paston, Terry Jones ya ce ya dage shirinsa bayan roko daga Gwamnatin Obama.

Barazanar ta sa ta haddasa zanga zanga mai tarzoma a Afghanistan.

Yansanda a can sun ce mutane 3 ne aka harbe, aka kuma raunata a lokacin daya daga cikin zanga zangar a wajen sansanin sojin kungiyar tsaro ta NATO.

A Pakistan masu zanga- zangar sun kona tutar Amurka. Shugaban Indonesia ya yi Allah wadai da shirin kona Al-Qura'anin a matsayin wata barazana ga zaman lafiyar duniya