Hare haren 'yan tawayen Uganda na barazana ga kuri'ar raba gardamar Sudan

Shugabannin siyasa da na addini a kasashen Afirka guda hudu wadanda ayyukan 'yan tawaye masu tada kayar baya ke kaiwa gare su, sun ce hare haren 'yan tawayen Uganda na Lord's Resistance Army ka iya matukar shafar kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a don samun yancin yankin kudancin Sudan.

Wakilan kasar Sudan da na Jamhuriyar Demokuradiyar Congo da Uganda da jamhuriyar Afirka ta tsakiya, sun ce kamata yayi Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatocin da abin ya shafa su tashi tsaye domin samar da tsaro ga fararen hula.

Sun yi wannan jawabi ne a karshen wani taron kwanaki ukku a kan kungiyar 'yan tawayen Lord's Resistance Army wanda aka yi a birnin Yambio dake kudancin Sudan.