Sabuwar Kungiyar mayakan sa kai a Columbia

A kasar Columbia, wata cibiya mai zaman kanta da ke yin nazari akan al'amuran yau da kullum a kasar, ta bayyana cewa wata sabuwar kungiyar masu fataucin miyagun kwayoyi dake dauke da makamai ta maye gurbin wadda aka kawar a shekarar 2006.

A wani nazari da cibiyar ta yi dangane da wannan al'amari, ta fahimci cewa kusan a dukkan lardunan kasar, masu fataucin miyagun kwayoyi dake dauke da makamai sune ke haddasa tashin hankali.

Kuma kawo yanzu, ana cigaba da hada hadar hodar ibilis a kasar.

Wannan kuma shine tushen duk wani tashin hankali da kasar ke fuskanta.